Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Yanzu-yanzu: Abduljabbar ya sanya sharaɗi ko ya fice daga Muƙabala

Published

on

Sheikh Abduljabbar Kabara ya sanya sharuɗa biyu domin ficewa daga Muƙabalar da ake tsaka da gudanarwa yanzu haka.

Malamin ya ce, ba zai ƙara amsa wata tambaya ba, matuƙar za a ci gaba a tsarin da aka shirya ta.

Tsarin Muƙabalar dai na bayar da mintuna biyar ɗin farko su yi tambaya sai a bashi minti goma domin ya amsa.

Daga nan kuma sai a ƙara sake bai wa kowane ɓangare dama domin ɗauraya.

Sharaɗi na biyu da ya sanya shi ne, matuƙar ba a amince masu ɗaukar bidiyo ɗin sa su naɗi muƙabalar ba, domin bai san waɗanda aka bai wa dama su ɗauka ba.

Ya ce, matuƙar ana kan waɗannan sharuɗa to ba zai amince ya sake amsa wata tambaya da aka yi masa ba.

Malam Kabara, ya zargi ma’aikatar harkokin addini da sauya salon muƙabalar saɓanin yadda aka shirya a baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!