Labarai
Yanzu-yanzu: An ci tarar Naira miliyan 5 ga wani kamfanin sarrafa ƙarfe a Kano

Kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli ta yanke hukuncin tarar Naira miliyan 5 ga wani kamfanin sarrafa ƙarfe a Kano.
Kazalika bayan tarar an rufe kamfanin nan take har sai an kammala bincike a kansa.
Yadda ma’aikatan kamfanin suka yi cirko-cirko
Alkalin kotun mai shari’a Auwal Yusuf ne ya yanke hukuncin da safiyar yau Asabar.
Exif_JPEG_420
Hukuncin ya biyo bayan samun kamfanin mai suna Yongxing Stell wanda mallakin ƴan ƙasar China ne da ke kan titin Hotoro Eastern by-passan yana aiki a lokacin da ake gudanar da tsaftar muhalli.
Tuni dai an rufe kamfanin tare da bada umarnin fara bincike a kansa.
You must be logged in to post a comment Login