Labarai
Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a wani gini dake Abuja
Jaridar Punch ta rawaito cewa gobarar ta tashi ne daga saman gini wanda ya sanya hayaki ya turnaki saman yankin baki daya.
Sai dai kawo yanzu ba a hangi jami’an kashe gobara ba a ginin, domin kokarin kashe wutar.
Gobarar ta tashi ne a cibiyar ciniki ta duniya dake birnin Abuja.
Tun a shekara ta 1939 New York na kasar Amurka, aka kafa cibiyar ciniki a duniya wanda take da rassa a kasashe 90 ciki har da jamhuriyyar Niger.
Muna dauke da cikakken labarin a labrun mu na gaba
You must be logged in to post a comment Login