Labarai
Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Kano ta ci tarar miliyan biyu ga yan kasuwar Singa
Gwamnatin jihar Kano yankawa shugabannin ‘yan kasuwar Singa tarar kudi miliyan 2.
Tarar tasu dai, ta biyo bayan rashin tsaftace kasuwar da suka yi na karshen wata nan.
Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bada umarnin cin tararsu, karkashin kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli.
Ya ce, an yanke hukuncin ne karkashin sashi na 27 a dokar kula da tsaftar muhalli ta shekarar 2016.
Tuni dai an aike musu da sammaci tare da bukatar su biya tarar kudi naira miliyan 2.
Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, wannan izina ce ga dukkan wata kasuwa da ta karya dokar tsaftar muhalli.
Kotun tafi da gidanka karkashin mai shari’a Auwal Yusuf Sulaiman ta bai wa shugabannin kasuwar wa’adin kwanaki uku da su tsaftace kasuwar.
You must be logged in to post a comment Login