Labarai
Yanzu-Yanzu: Kamfanin Twitter ya rubuto wa Najeriya wasikar neman sulhu
Gwamnatin tarayya ta ce kamfanin Twitter ya rubuto wa Najeriya wasika yana buƙatar da a zauna a teburi don sasanta saɓani da ke tsakanin kasar nan da twitter wanda yayi sanadiyar gwamnatin tarayya ɗaukar matakin dakatar da kamfanin daga gudanar da harkokinsa a ƙasar nan.
Ministan yaɗa labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammed shine ya bayyana haka a cikin wani shiri na gidan radio Najeriya da ya gudana da safiyar yau talata.
‘‘Ina tabbatar muku cewa kamfanin Twiiter ya rubuto mana wasika yana neman a sasanta’’
‘‘Kuma mu dama tun farko mun ce kofar mu a buɗe take a koda yaushe za mu iya sauraran masu neman sasantawa’’ a cewar sa.
Ministan ya kuma ƙara jaddada matsayin gwamnati da ke cewa, ba za ta lamunci duk wani kamfani ko na cikin gida ko na ketare da zai tada zaune tsaye a ƙasar nan ba.
A cewar ministan gwamnati ta gindaya wa kamfanin na Twitter ka’idoji wadda ta ce sai ya amince da su kafin a bashi damar gudanar da ayyukansa a Najeriya. Cikin ƙa’idojin akwai batun sanin labaran da za a rika wallafa a shafin na twitter, sannan wajibi ne kamfanin na Twitter da duk wani kamfanin na ketare ya tabbata yayi rajista da hukumar kula da kafafen yada labarai ta Radio da talabijin ta kasa kasa (NBC)
You must be logged in to post a comment Login