Labarai
Yanzu-yanzu: Kungiyoyin NLC da TUC sun bayyana ranar da zasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

Kungiyar kwadagon ta Nijeriya da kungiyar ‘yan Kasuwa a sun bayyana ranar 3 ga watan Oktoba mai kamawa dai-dai da ranar Talata a matsayin ranar da zasu shiga yajin aikin sai baba ta gani a fadin Kasar.
Hakan dai ya biyo bayan shiga wata tattaunawar da kungiyoyin suka Yi na musamman kan batun tafiya yajin aiki sai baba ta gani a kasar da misalin karfe 3 na ranar yau Talata.
A dai ranar 5 da 6 ga watan Satumabar nan da ake ciki ne kungiyar kwadagon ta yi yajin aiki gargadi na kwanaki biyu, don tilastawa gwamnati kawo karshen wahal-halun da al’ummar kasar ke fuskanta.
You must be logged in to post a comment Login