Labarai
Yanzu-yanzu: Majalisar dokoki ta amince Ganduje ya ciyo bashin Naira Biliyan 10

Majalisar dokokin jihar Kano, ta amincewa gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ciyo bashin naira biliyan goma.
Kuɗaɗen da za a ciyo bashin, za a yi amfani da su wajen sanya na’urorin CCTV domin kyautata tsaro a jihar.
Amincewar ciyo bashin ta biyo bayan wasiƙar da gwamnan ya aikewa majalisar wadda shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta a zaman majalisar na ranar Laraba.
Ta cikin wasiƙar gwamna Ganduje ya ce, za a sanya na’urorin ne la’akari da barazanar tsaro da jihar ke fuskanta a ƴan kwanakinnan.
Wakilin Freedom Radio a majalisar Auwal Hassan Fagge ya ruwaito cewa, bayan tattauna batun ne tare da bada shawarwari ƴan majalisar suka amince a ciyo bashin.
You must be logged in to post a comment Login