Labarai
Yanzu-yanzu: Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan ya rasu
Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan ya rasu.
Rahotanni daga iyalan Marigayin sun bayyana cewa ya rasu da safiyar yau Juma’a bayan wata gajeriyar rashin lafiya.
An haifi Alhaji Mukhtar Adnan a shekarar 1926 kuma tsohon sarkin Kano Sir Muhammad Sanusi ne ya naɗa shi a matsayin sarkin Bai a shekarar 1954 domin ya gaji mahaifinsa Sabon Dambazau.
Marigayi Sarkin Bai shi ne kwamishinan ilimi na farko a jihar Kano a 1968, kuma halarci makarantar Elementary da ke Ɗanbatta da makarantar Midil ta Kano da kuma makarantar malamai a garin Zaria.
Jama’ar Musulmi na alhinin rashin Malam Mas’ud Hotoro
Marigayin ya kasance tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya a jamhuriya ta farko, kuma guda daga cikin mamba mafi daɗewa a majalisar masarautar Kano masu zaɓen sarki tsawon shekaru 63.
Kuma yana cikin waɗanda suka zaɓi sarakuna da suka haɗar da Sarkin Kano Muhammadu Inuwa a 1963, Sarkin Kano Ado Bayero 1963 zuwa 2014, sai Sarkin Kano Muhammad Sanusi 2014 da Sarkin Kano Aminu Bayero a 2020.
Za a yi jana’izar sa a garin Ɗanbatta bayan saukowa daga masallacin Juma’a.
You must be logged in to post a comment Login