ilimi
Yara miliyan daya ba sa zuwa makaranta a Kano- UNICEF
Wani rahoton da asusun tallafawa kananan yara na majalisar Dinkin duniya ya fitar a shekarar da mukayi bankwana fa ita ta 2022, ya nuna cewa kimanin yara miliyan goma da dubu dari biyar ne ba sa samun damar zuwa Makaranta a fadin duniya.
Sai dai kuma rahoton ya nuna cewa akasarin yaran da basa zuwa makarantar sun fito ne daga Najeriya.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake bikin ranar ilimi ta duniya a yau 24 ga watan Junairu.
Majalisar Dinkin duniya ce dai ta Saba gudanar da bikin duk shekara domin lalubo hanyoyin gyara a fannin na ilimi.
Danna alamar sauti domin jin cikakken rahoton.
Rahoton:Hafsat Abdullahi Danladi.
You must be logged in to post a comment Login