An Tashi Lafiya
Yarima Faisal Bin Farhan ya ziyarci shugaban Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin Yariman ƙasar Saudiyya kuma Ministan harkokin ƙasashen waje, Yarima Faisal Bin Farhan Al-Saud a fadar sa, a ranar Talata.
Wata sanarwa da fadar ta fitar tace, Shugaba Buhari ya shaida wa Yariman cewa, Najeriya ƙasa ce mai ɗumbin jama’a kuma ga abubuwan more rayuwa, ya kuma ce ƙasar Najeriya na dogaro ne da arzikin man fetur domin samun kuɗaɗen shiga.
Shugaba Buhari, ya kuma ƙara da cewa Saudiyya na kyautata wa ƙasar nan, ta hanyar rage man da ta ke siyarwa ƙasar nan a lokuta da dama.
Shi ma Yarima Al-Saud, ya miƙa saƙon gaisuwar Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud ga Buhari, yana mai cewa “Saudiyya ta yaba da alaƙarta da Najeriya ta tsawon shekara 61 kenan, kuma tana fatan ɗorewar ta.” kamar yadda BBC suka rawaito.
You must be logged in to post a comment Login