Labarai
Yau ake bikin ranar aikewa da sakonni ta duniya
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 9 ga watan Octoban kowacce shekara a matsayin ranar aikewa da sokkonni ta duniya da nufin bunkasa hanyoyin aikewa da sakkonni cikin sauki.
Majalisar dinkin duniya dai ta kaddamar da ranar ne da nufin farfado da hanyoyin aikewa da sakonni da suka fara bacewa watakila a dalilin wayoyin hannu da kuma bullowar kafafen sada zumun ta na zamani.
An kuma fara bikin ranar ne tun a shekarar 1969 a birnin Tokoyo na kasar Japan.
You must be logged in to post a comment Login