Labarai
Yau Malam Aminu Kano ke cika shekaru 38 da rasuwa
An haifi Malam Aminu Kano a ranar 9 ga watan Augusta 1920 a unguwar Sudawa da ke yankin karamar hukumar Gwale a birnin Kano.
Malam Aminu Kano ya halarci kwalejin Katsina kafin daga bisani ya zarce zuwa sashen nazarin ilimi da ke jami’ar London shi da tsohon firaministan Najeriya, Sir Abubakar Tafawa Balewa.
Malam Aminu Kano ya samu takardar shaidar koyarwa a jami’ar London, inda ya zama malami ya kuma koyar a kwalejin horas da malamai da ke Bauchi.
Lokacin da ya ke koyarwa a Bauchi ya shahara wajen sukar salon mulkin turawan mulkin mallaka.
A shekarar 1943 shida Sa’adu Zungur da Abubakar Tafawa Balewa suka kafa wata kungiyar siyasa da ake wa lakabi da BAUCHI Bauchi General Improvement Union.
A shekarar 1948 ne kuma ya zama shugaban makarantar Maru da ke jihar Sokoto sannan aka zabe shi a matsayin sakataren kungiyar malaman arewacin Najeriya.
Lokacin da ya ke zaune a Sokoto ya ba da gudunmawa wajen bunkasa ilimin Qur’ani a makarantu.
Haka kuma a Sokoton ne ya shiga Jam’iyyar Mutanen Arewa, wanda ita ce daga bisani ta rikide ta zama jam’iyyar NPC.
Malam Aminu Kano ya balle daga jam’iyyar NPC, inda shi da wasu ‘yan gwagwarmaya suka kafa jam’iyyar NEPU.
You must be logged in to post a comment Login