Labarai
Daliban da Boko Haram ta sace sun cika shekaru 9 a hannunsu
A yau ne aka cika shekara tara da sace daliban makarantar sakandiren mata ta Chibok da ke Maiduguri a jihar Borno su dari biyu da saba’in da shida, tun a shekarar 2014.
Wasu yan kungiyar boko haram ne suka sace su, a cikin daren ranar 14 ga watan Afrilu.
Rahotanni sun nuna cewa, har yanzu akwai sauran daliban cChibok kimanin 96 da suka rage a hannun ‘yan bindigar Kuma an gaza samo inda aka boye su.
Sannu a hankali dai wasu daga cikin daliban suka rika samun hanyar tsira suna guduwa cikin gari, sai dai mafi yawan su suna dawowa dauke da juna biyu wasu Kuma da goyon yara a tare da su.
A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne dai ‘yan Boko Haram din suka mamaye Makarantar sakandiren ‘yan mata ta Gwamnati dake garin Chibok a Jihar Borno.
Bayan sace ‘yan mata ne gwamnati da jami’an tsaro a kasar suka fara kokarin ganin sun kubutar da daliban daga hannun ‘yan Boko Haram, har ma aka jiyo Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cewa ‘ na bada tabbacin cewa bai manta da daliban Chibok da aka sace, kamar yadda iyayensu suke ji.
Har yanzu dai iyayen sauran daliban na cigaba da fafutikar ganin ‘ya ‘yan nasu sun kubutar, musamman yadda suke bayyana bakin cikinsu a zantawarsa daga manema labarai.
Inda har yanzu ake kyautata zaton akwai ‘yan mata 96 da suka rage a hannun ‘yan bindigar, Daya Sanya kungiyoyin ke cigaba da fafutuka don ganin an kubutar da sauran ‘yan matan da suka rage don ganin an kubutar dasu.
You must be logged in to post a comment Login