Labarai
Yau shekara 20 da rasuwar Mamman Shata -Tarihin Rayuwarsa
An haifi marigayi Dr. Mamman Shata a shekarar 1923 a Jihar Katsina a garin Musawa yayi kaura zuwa garin kano ya kuma rasu a ranar 18 Yunin Shekarar 1999 an binne shi a garin Daura kamar yadda yabar wasiya
Yana da wakoki wanda har ya zuwa yanzu ba’asan adadinsu ba dan shi kansa da aka tambayeshi cewa yayi baisan adadin wakokinsa ba amma a shekarun baya an sami wata baturiya data zo dan tattara wakokinsa inda ta fitar da kididdigar sun kai dubu hudu. Kuma mawakine da yake da abin mamaki kwarai da gaske yakanyi waka duk lokacin da aka so hakan batareda inda-inda ba.
An taba tambayar Dr Mamman shata dalilin dayasa ya fara waka amsar daya bayar shine dalilin kiriniya ta yarinta kurum, bawai don gadon uwa ko uba ba, domin kuwa na dade ina yi bana kabar ko anini, in ma an samu kudi sai dai makada da maroka su dauka. Sai daga baya bayan na mai da waka sana’a na fara karbar kudi.
Bisa al’ada ga yanda mawakan Hausa suke yin wakokin su, akwai waka da suke yi wa kansu da kansu kirari a cikinta wadda aka fi sani da suna Bakandamiya. To shima Marigayi Dr. Mamman Shata bai yi kasa a guiwa ba wajen yi wa kansa irin wannan waka.