Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yau Shugaba Buhari zai yi jawabi a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya

Published

on

A Yau juma’a ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi a zauren taron majalisar dinkin duniya karo na 76 da ake gudanarwa a birnin New York na ƙasar Amurka.

Shugaba Buhari zai yi jawabin na sa ne da misalin ƙarfe 2 rana, mai taken ‘zauren da kuma ƙalubalen da suka addabi duniya.

Ana sa ran wasu shuwagabinin ƙasashen za su gabatar da na su jawabin da suka haɗar da shugaban Jamhuriyar Benin, da na Sudan da senegal da kuma Jamus da Gambia da dai sauransu.

kafin gabatar da Jawabin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da wasu shugabanin ƙasashen duniya ciki har da shugaban kasar Burundi, da Shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya, Ngozi Okonjo-Iweala.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!