Connect with us

Labarai

Yawan kisan da ake yi a Najeriya ya yi yawa – CAN

Published

on

Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta ce matsalar rashin tsaro da kashe-kashen da ke faruwa a ƙasar ba Kiristoci kaɗai ta shafa ba, domin Musulmai da Kiristoci duka suna fuskantar irin wannan barazana.

Shugaban ƙungiyar ta arewa, Rabaran Joseph Hayab, ya bayyana haka yayin da yake bayani kan matakin da CAN ta ɗauka na ayyana kwanakin jimami na ƙasa tare da kira ga gwamnati ta ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro.

A makon nan ne CAN ta sanar da ayyana ranakun jimami na ƙasa daga ranar 12 ga Yuni, 2026, tare da ayyana ranar Lahadi 14 ga Yuni a matsayin baƙar Lahadi “Black Sunday” a dukkan majami’un Najeriya domin tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare da tashin hankali a sassan ƙasar.

Matakin ya biyo bayan taron shugabannin mabiya addinin kirista da aka gudanar a Abuja.

Da yake amsa tambayar dalilin da ya sa ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki yanzu duk da cewa an daɗe ana fama da matsalar tsaro a jihohi kamar Borno da Kebbi, Hayab ya ce lamarin ya kai matakin da ba za a iya ci gaba da yin shiru a kansa ba.

“Kashe-kashen ya yi yawa, dole ne mu fita mu nemi mataki. Ba wai akwai wanda Allah ya halitta da ya fi wani ba. Duk sace-sacen da aka yi a baya da waɗanda ake yi yanzu sun shafi ‘yan Najeriya ne, Musulmai da Kiristoci,” in ji shi.

Jami’in na CAN ya kuma yi zargin cewa tun farko shugabanni da ‘yan ƙasa sun kasa fuskantar ainihin matsalar yadda ya kamata. A cewarsa, maimakon mayar da hankali kan magance matsalar, mutane sun shafe lokaci suna musayar zargi da musanta abin da ke faruwa.

Ya ce yanzu lamarin ya kai matsayin da kowa ya fahimci girman barazanar da ke tattare da shi.

“Wuta ce da za ta cinye mu gaba ɗaya da gidan talaka da na mai kuɗi da gidan Arewa da na Kudu da gidan Kirista da na Musulmi. Wannan abu ne da ya shafi kowa da kowa,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga Musulmai da sauran ‘yan Najeriya da su haɗa kai wajen neman mafita ga matsalar tsaro, yana mai cewa ba batun CAN kaɗai ba ne.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!