Labarai
Masu garkuwa da mutane sun sace ƙanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki

Wasu mahara da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi sace ƙanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, tare da ‘ya’yanta tagwaye biyu a birnin Badun na Jihar Oyo.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau Laraba a unguwar Elewura da ke yankin Challenge, a ƙaramar hukumar Badun ta Kudu.
Mai taimaka wa Adelabu a harkokin yaɗa labarai, Femi Awogboro, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ƙanwar Adelabu tare da tagwayen nata, Peter da Paul, sun fito daga gida lokacin da wasu ‘yan bindiga suka tare su tare da yin garkuwa da su.
A cewarsa, maharan sun kai harin ne ba zato ba tsammani kafin su tafi da waɗanda suka sace zuwa wani wuri da ba a sani ba.
A watan Mayun da ya gabata an yi garkuwa da malamai da ɗalibai sama da 40 a yankin Ahoro-Esiele na ƙaramar hukumar Oriire, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce kan matsalar tsaro a jihar.
You must be logged in to post a comment Login