ilimi
Za a ƙaddamar da irin wake mai bijirewa ƙwari a watan Yuli a Kano – farfesa Abdullahi Mustapha
Hukumar bunƙasa fasahar inganta tsirrai da dabbobi ta ƙasa wato National Biotechnology Development Agency, za ta ƙaddamar da wani sabon nau’in wake da ke bijirewa ƙwari dangin ‘Maruca’ a watan gobe na Yuli anan Kano.
Shugaban hukumar farfesa Abdullahi Mustapha shine ya bayyan haka yayin zantawa da manema labarai, jim kaɗan bayan kammala taron bita na kwanaki biyu da hukumar ta shirya a Kano.
‘‘Nau’in waken da akewa lakabi da (bt cowpea) yana da kariya da zai rika bijewa illar da ƙwari, musamman waɗanda ake kira da MARUCA’’ a cewar sa.
‘‘Najeriya kasa ce da ta ke da ɗumbin arzikin filin noma amma saboda rashin mai dahankali da kuma bin hanyoyin kimiyya ya sanya kasashe da dama sun yiwa kasar nan fintakau’’.
‘‘Saboda haka manoman mu musamman na nan arewa su rungumi sabon irin waken na bt cowpea da zaran an fitar da shi kasuwa don samun amfanin gona mai yawa’’ inji farfesa Abdullahi Mustapha.
A nasa ɓangaren mataimakin gwamnan jihar Kano Dr Nasir Yusuf Gawuna wanda mai bai wa gwmanan Kano shawara kan harkokin noma, Hafiz Muhammed ya wakilta, ya ce, gwamnatin Kano ta rungumi bin hanyoyin kiimiyya musamman fasahar Biotechnology don bunƙasa harkar noma a jihar.
‘‘Gwamnati za ta ci gaba da wayar da kan manoma don ganin sun ci gajiyar sabbin iri da hukumar NABDA za ta ƙaddamar anan Kano a watan gobe’’ a cewar sa.
Madam Rose Giɗaɗo ita ce babbar jami’ar shirin bunƙasa noma ta hanyar amfani da fasahar Biotechnoloy a nahiyar, anan Najeriya, ta ce, an shirya taron ne da nufin wayar da kan masu ruwa da tsaki game da muhimmancin bin ha nyoyin kimiyya don bunƙasa noma a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login