Connect with us

Labarai

An sanya ranar bude makarantun Firamare da Sakandire a Legas

Published

on

Gwamnatin jihar Lagos ta bayar da umarnin bude makarantun Firamare da sakandare na gwamnati da kuma masu zaman kansu a ranar 21 ga watan nan da muke ciki na Satumba, don fara sabon zango na shekarar karatu ta 2020/2021.
Kwamishiniyar ilimi ta jihar Folasade Adefisayo ce ta bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ta fitar yau mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Kayode Abayomi.
Sanarwar ta ce kowa da kowa ne zai koma makarantun firamare da sakandaren na masu zaman kansu, yayin da a makarantun gwamnati kuma aji uku na karamar sakandare da aji biyu na babbar sakandare ne za su koma.
Kwamishiniyar ta kara da cewa nan gaba kadan za a duba yiwuwar komawar sauran daliban na makarantun firamare da sakandaren gwamanti a Jihar ta Lagos.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,987 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!