Jigawa
Za a kafa dokar hukuncin kisa ga masu fyaɗe ba tare da zaɓin tara ba a jihar Jigawa
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kafa dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin yi wa ƙaramar yarinya fyaɗe, a wani mataki na tabbatar da kare kananan yara.
Kwamishinan harkokin shari’a na Jihar Dr Musa Adamu ne ya sanar da hakan jiya, yayin taron manema labarai na ƙarshen shekara da ya gudanar a birnin Dutse.
Dr Musa Adamu ya ce duk wanda aka kama da yi wa ƙaramar yarinya ‘yar ƙasa da shekaru goma fyade a jihar to haƙiƙa hukuncin kisa ya tabbata a kansa, ba tare da zaɓin ɗaurin rai-da-rai ba.
Tun a farkon shekarar nan ce gwamnan Jihar ta Jigawa Alhaji Muhammad Badaru ya sanya hannu kan dokar kare kananan yara, wadda ta yi tanadin hukuncin kisa kan masu fyaden, amma kuma da zabin daurin rai-da-rai.
You must be logged in to post a comment Login