Labarai
Za a samu tsananin zafi a wasu jihohin Arewa- NiMET
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMET, ta bayyana cewa, akwai yiyuwar mazauna birnin tarayya Abuja da Kano da kuma sauran jihohin Arewa da dama su fuskanci tsananin zafi wanda zai shafi lafiyarsu.
Haka kuma, a cewar hukumar al’ummar jihohin da za a yi wannan zafi ka iya fuskantar matsanancin zafi, wanda zai sa su shiga yanayi mara kyau.
Hukumar ta ce, “Ya kamata jama’a su ɗauki matakan da suka dace domin kare kai da kuma kula da lafiyarsu”.
Ka zalika ta kara da cewa, Abuja da Kano da Sokoto da kuma Kogi ne za su fi fuskantar tsananin zafi, inda ta shawarci mazauna yankunan da su ɗauki matakin kariya da ya kamata.
Karin jihohin da za su fuskantaci zafin sun haɗa da Kebbi da Katsina da Adamawa, sai Gombe da Bauchi da Taraba da Neja da Zamfara da Nasarawa da Jigawa da Benue da kuma Kwara.
Haka kuma hukumar ta NiMET ta gargaɗi mazauna jihohin Osun da Ekiti da Ondo da Bayelsa da Akwa Ibom da Anambra da Delta da Enugu da Edo da Ogun da Plateau da Borno da Imo da Abia da Cross River da cewa su kasance cikin shiri don karuwar zafi, duk da cewa zafin ba zai yi tsanani ba kamar na sauran jihohi.
You must be logged in to post a comment Login