Labarai
Za a yiwa masu rike da madafun iko gwajin taamali da kwayoyi
Gamayyar kungiyoyin lafiya JUHESU sun rubutawa ministan kwadago da samar da aikin yi Dakta Chris Ngige wasikar buƙatar bai wa manbobin su abubuwan da suke bukata.
JOHESU sun rubuta wasikar ne a ranar 10 ga watan satumba 2021 bisa zargin kungiyar likitoci ta kasa NMA da yin katsa-landan a cikin Al’amuran ta.
Gamayyar kungiyoyin sun aikewa gwamnatin tarayya cewa, a kowanne bangare na aikin gwamnati walwalar ma’aikata abin bukata ne kuma shi ne a gaba da komai.
Wasikar ta JUHESU mai dauke da sa hannun shugaban ta kwamared Bio Josiah wani bangare ne na sake tunatar da gwamnatin tarayya kan barazanar tsunduma yajin aiki da suka yi kafin wa’adin kwanaki 15 da suka bayar.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kungiyar NMA ta gana da shugaban kasa Muammadu Buhari.
You must be logged in to post a comment Login