Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu ɗau mataki ga duk wanda muka samu da tada hankalin al’umma – Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin sa bazata lamunci barin duk wasu wanda zasu kawo barazanar tsaro a fadin jihar ba, inda gwamnan yace za’a dau matakin ba sani va sabo ga duk wanda aka kama da aikata laifi a yayin bukukuwan sallah.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin da sarkin kano Alhaji Áminu Ado Bayero ya kawomai ziyara cikin wani ɓangare na bikin sallah ƙarama.

Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa gwamnati zata tabbatar da ta samarwa da al’umma kyakkyawan tsaro a faɗin jihar.

Da yake jawabi tun da fari sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yabawa gwamnatin bisa yadda ta bayar da tallafin kayan abinci ga al’ummar jihar a lokacin watan azumin Ramadana domin saukakawa al’umma.

Haka kuma gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci al’umma da su mayar da hankali wajen sanya idanu ga al’umma domin samar da tsaro a fadin jihar dama ƙasa baki ɗaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!