Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu ɗaukaka ƙara kan hukuncin Kotu- Engr Abba Kabir Yusuf

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, za su bi matakin ɗaukaka ƙara zuwa gaba domin tabbatar da adalci kan hukuncin da kotu ta yanke a yau Laraba da ta ayyana abokin karawarsa Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaɓen bana.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da ya gudanar a fadar gwamnatin jihar a daren nan.

Ya ƙara da cewa, “Mun umarci lauyoyin mu da su hanzarta wajen ɗaukaka ƙara ba tare da ɓata lokaci ba”.

Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma ce, wannan hukunci ba zai sanyar musu da gwiwa ba wajen ci gaba da gudanar da ayyukan da suka fara.

Haka kuma ya, gwamnatinsa ta tabbatar da cewa hukuncin da aka yanke an yi shi ne bisa son zuciya, inda suke fatan kotun gaba za ta yi duba na tsanaki tare da tabbatar da gaskiya.

Rahoton: Umar Abdullahi Sheka

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!