Labarai
Za mu baza jami’ai 1,500 don tabbatar da doka a bikin Sallah- KAROTA
Hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta jihar KAROTA, za ta baza jami’anta guda 1,500 domin sanya ido a shagulgulan bikin Sallah.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya fitar yau Litinin.
Ta cikin sanarwar, hukumar ta KAROTA, ta ce, za ta rarraba jami’an nata ne domin su tabbatar da bin dokokin tuki a yayin bukukuwan na Sallah.
Haka kuma hukumar ta ja hankalin jama’a da su kiyaye tare da bin doka sau da ķafa domin guje wa hadura a lokacin bikin Sallah.
Hukumar ta ce, ta haramta yin guje-guje da ababen hawa da wasu ke yi, wadanda hakan ke zama barazana ga rayuwar al’umma
KAROTA, ta kuma ja hankalin iyaye da su guji bai wa yaran da suke kasa da shekaru 18 tukin ababen hawa, domin kuwa hukumar ba za ta lamunci hakan ba.
You must be logged in to post a comment Login