Labarai
Za mu baza jami’anmu don sanya ido kan masu yin bukukuwan Maulidi- Hisbah

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce, za ta ba za jami’anta a ko ina a fadin jihar don tabbatar da cewa ana gudanar da bukukuwan Mauludi cikin kwanciyar hankali kuma yadda ya dace.
Mataimakin shugaban hukumar Dakta Mujahiddeen Aminudden, ne ya bayyana hakan ta cikin wata murya da ya aiko wa Freedom Radio.
Wanda ya ce, a irin wannan lokaci wasu mutanen na fakewa da bikin na Maulidi su na yin wasu abubuwan da ba su dace ba, shi ya sa za su baza jami’an na su domin tabbatar da ana gudanar da bikin yadda ya dace.
You must be logged in to post a comment Login