Labarai
Za mu dauki ma’aikata sama da 4000 don sarrafa shara a Kano – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da tabbatar da kudirinta na tabbatar da jihar ta kasance cikin tsafta da tsafta da nufin ci gaba da kasancewar ta a matsayinta na babban birni ta hanyar inganta shara don mayar da ita dukiya.
Kwamishinan muhalli na jihar Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya bayyana hakan yayin da yake duba wasu kayayyakin aiki na ma’aikatar a wani bangare na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da wani kamfanin kula da shara mai zaman kan sa.
Getso ya ce, kasashen da suka ci gaba a Duniya sun samu dumbin arziki daga shara, a don haka jihar Kano za ta bi sahun su don cin gajiyar tsarin, don kuwa jihar Kano na daya daga cikin wuraren da ake da dumbin shara.
Dakta Getso, ya ci gaba da cewa yarjejeniya da kamfanin za ta dauki tsawon shekaru ashirin, kuma zai bada damar daukar ma’aikata dubu hudu da dari biyar a a cikibiyoyin sarrafa shara guda uku da ake da su a kano, wanda ya hada da kamfanin Dorayi Composing, Kawo bio-gas da kuma Zaura.
You must be logged in to post a comment Login