Labarai
Za mu gina sabon gidan marayu da makarantar musabaƙar Alƙur’ani- Gwamna Abba

Gwamnatin jihar Kano, ta ce, ta kammala shirin gina sabon gidan marayu tare da kafa makarantar da za a riƙa gudanar da gasar musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa, a wani mataki na bunƙasa ilimin addini da tallafa wa marayu da masu ƙaramin ƙarfi a jihar kano dama ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin bikin rufe gasar musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa da gwamnatin jihar ta dauki nauyinta a birnin Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafawa irin waɗannan shirye-shiryen saboda rawar da suke takawa wajen bunƙasa tarbiyya da ilmantarwa a tsakanin matasa.
Zainab Aminu yar asalin jihar Borno ce ta lashe gasar, a bangaren mata, ta bayyana farin cikinta bisa samun nasarar tare da shan alwashin kara dagewa musamman ma a fannin karatun a fannin ci gaban addinin Musulunci.
Gwamnan ya bai wa dukkan waɗanda suka yi nasara Abdulkarim Mustapha daga jihar Zamfara da Zainab Aminu daga Borno kyautar kuɗi naira miliyan ɗaya da rabi kowannensu tare da kujerun aikin Hajji, a matsayin ƙarfafa gwiwa ga ci gaba da jajircewa wajen gudanar da karatun Alƙur’ani mai girma.
You must be logged in to post a comment Login