Labaran Freedom
Za mu kama wadanda suke gudun wuce sa’a a titunan Kano – FRSC
- Za mu dau hukuncin kan wanda muka kama yana gudun wuce sa’a a titunan Jihar Kano
- Yawancin hadduran da akeyi suna faruwa ne sakamakon gudun wuce sa’a.A bi doka don gujewa
- Abinda ka iya zuwa ya dawo.
Hukumar kiyaye afkuwar hadura a Nigeriya reshen jihar kano ta ce, za ta dauki mataki mai tsauri a kan duk wanda ta kama yana yin gudun wuce sa’a akan titunan jihar Kano.
Mai magana da yawun hukumar ta FRSC Abdullahi Aliyu Labaran ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio
Wanda ya ce, ‘babban abinda ke kara haifar da haddura a wasu daga cikin titunan jihar, bai wuce gudun wuce sa’a ba, da kuma rashin bin dokokin yin tuki’.
Abdullahi Labaran ya ce ‘hakan ne yasa wajibi hukumar ta dauki matakin dakile wannan matsalar, ta hanyar kama wandanda suke gudun wuce sa’ar, tare da hukunta su’.
Sai dai kuma ya ce ‘ yana fatan masu irin wannan dabi’ar zasu daina, don tsiratar da rayukansu, dana al’umma baki daya.
RAHOTO: Halima Wada Sinkin
You must be logged in to post a comment Login