Kiwon Lafiya
Za mu mayar da asibitoci yin aikin Sa’o’i 24- Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta ce, za ta tabbatar da cewa, ta mayar da dukkan asibitocin faɗin jihar zuwa yin aiki na tsawon sa’o’i 24.
Kwamishina lafiya Drakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin bude taron kara wa ‘yan jarida sani kan hanyoyin da za a bi wajen inganta kananan asibitocin da ake da su a Kano.
Kwamishinan, ya kuma ce gwamnatin Kano za ta hada hannu da manema labarai wajen ganin ta bunkasa bangaren kiwon lafiya.
Da yake jawabi yayin bude taron, shugaban kungiyar da ta shirya taron wadda ke rajin kare lafiyar mata da kananan yara mai suna Engender Health, Malam Abdulaziz Jumare, ya bayyana cewa ta hanyar bayar da labarai ingantattu musamman ma a fannin lafiya daga ‘yan jaridu zai taimaka wajen samar wa bangaren lafiya ci gaba a jiharKano.
Yayin taron wanda ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta shirya da hadin gwiwar kungiyoyin rajin kare lafiya ta Engender Health da kuma ISMPH, za a shafe tsawon kwanaki uku ana gudanar da shi.
You must be logged in to post a comment Login