Labarai
Za mu sabunta matakan kare manhajojin sadarwar al’umma – NCC
Hukumar lura da kafafen sadarwa ta ƙasa NCC, za ta sabunta matakan kare manhajojin sadarwar al’umma.
A wani mataki na kare bayanan al’umma da kuma faɗawa hannun ƴan damfara.
Shugaban sashen lura da ayyukan al’umma na hukumar NCC Mista Efosa Idehen ne ya bayyana haka a ranar Juma’a yayin taron wayar da kan al’umma kan kare bayanan su.
Taron wanda aka yiwa take da “Buɗe Idonka, kar ka faɗa tarkon ƴan damfara” an gudanar da shi a gidan Mumbayya da ke Kano.
Mista Edehen wanda Hajiya Hafsat Lawan ta wakilta, “Yace yawaitar satar bayanai da kuɗaɗen al’umma yasa hukumar mu ta haɗa kai da babban bankin Ƙasa CBN, da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC da ICPC”.
“Sannan mun haɗa kai da rundunar ƴan sanda ta ƙasa don ganin an kawo ƙarshen matsalar masu satar bayanan al’umma” a cewar Edehen.
Shi ma a nasa jawabin daraktan kafafen yaɗa labarai na zamani da samar da tsaro na hukumar Dakta Haru Alhassan ya ce “Ana samun rahotannin masu kutse domin satar bayanan al’umma a don haka ya buƙaci jama’a da su daina bada bayanan su ga waɗanda ba su sa ni ba”.
NCC ta buƙaci masu amfani da katin cirar kuɗi na zamani ATM, da manhajar hada hadar Bankuna ta NIBBS, da su tabbatar da kare bayanan su da sirranta shi don kaucewa masu damfara da a kullum suke fito da sabbin dabarun satar kuɗaɗe da bayanan al’umma.
Yayin taron al’umma da dama musamman masu sana’ar hada-hadar kuɗi sun halarta kuma sun amfana da abinda aka koya musu.
You must be logged in to post a comment Login