Labarai
Za mu samar da asusun bunkasa ayyukan Noma a Najeriya – Majalisar dattijai
Majalisar dattijai ta amince da kafa asusun bunkasa ayyukan Noma na kasa da nufin samar da kudi don tallafawa dabarun bunkasa harkokin noma a Najeriya.
Wannan dai ya biyo bayan gabatar da rahoto da kwamitin majalisar dattijai kan harkokin Noma da raya karkara yayi a zaman majalisar na ranar Laraba 24 ga watan Maris 2021.
Shugaban kwamitin Sanata Abdullahi Adamu ne ya gabatar da rahoton tun da farko, inda ya bukaci a sake karanta kudirin a karo na biyu, wanda ya samu karatu na farko tun a ranar 4 ga Maris na shekarar 2020.
A cewarsa, kudirin na neman bunkasa ayyaukan noma tare da samar da kudade domin tallafawa bangaren a kasar nan, domin tabbatar da samar da abinci da wadatarsa a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login