Labarai
Za mu shiga tsakanin kamfanin UMZA da asibitin Yusuf Maitama Sule – Gwamanatin Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta shiga tsakanin kamfanin sarrafa shinkafa na UMZA da asibitin koyarwa na Yusuf Maitama Sule da ke kwanar Dawaki.
Wannan dai ya biyo bayan ƙorafin da mahukuntan asibitin koyarwa na Yusuf Maitama Sule suka yi kan yadda kamfani ke damun su da ƙurar shinkafa.
A ziyarar gani da ido da tawagar tsaftar muhalli ta kai kamfanin a ranar Juma’a ƙarƙashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar Adamu Abdu Faragai ya ce “Za mu shirya zama tsakanin kamfanin da asibitin don tattaunawa tare da gano inda matsalar take don sasantawa”.
“Gaskiya a yadda muka zagaya muka ga kamfanin ba mu tarar da wata matsala da za a yi ƙorafi a kanta ba, amma duk da haka za mu tattatauna da su don samar da daidaito” a cewar Faragai.
Adamu Abdu Faragaibya ci gaba da cewa “Mun tattauna da shugaban kamfanin ya kuma nuna mana wani ɓangare da suka ware da za su yi wata cibiya da za ta riƙa killace dusar shinkafar ba tare da ta damu kowa ba.
Ko da yake nasa jawabin shugaban kamfanin Aliyu Abubakar Ali ya ce, tun bayan yawaitar ƙorafin mahukuntan asibitin suka ɗauki matakin magance matsalar ta hanyar samar da cibiyar tattara dusar Shinkafar.
“Mun sani Matsalar da suke fuskanta bai kai su yi ƙorafin da suke yi ba, amma duk da haka a shirye muke mu amsa gayyatar da gwamnati za ta yi mana don tattaunawa da su kan matsalar.
Haka kuma tawagar tsaftar muhallin ta ziyarci kasuwar ƴan Lemo da ke Na’ibawa inda ta buƙaci shugabannin kasuwar da su mayar da hankali wajen daina tara shara a kasuwar don kare lafiyar su da ta abokan cinikin su.
Har ma ma’aikatar muhallin ta ci gaba da bibiyar kasuwar don tabbatar da sun bi ƙa’idojin tsaftar muhalli.
Tawagar tsaftar muhallin ta zagaya sassa daban daban na kasuwar don ganin halin da take ciki tare da basu umarnin yin gyara a wuraren da suke da matsala.
You must be logged in to post a comment Login