Labarai
Za mu soke rijistar kamfani dake satar suna a kasar nan – SON
Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa SON ta ce ba za ta saurarawa kamfanoni da sauran ‘yan kasuwa masu amfani da jabun kayayyaki da ma sauran kaya marasa inganci a cikin al’ummar kasar nan ba.
Babban daraktan hukumar Malam Faruk Salim ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyara daya kai wa kungiyar hadin kai ta kasuwar kasa da kasa dake Alaba a ofishinta dake birnin Ikko.
Malam Faruk Salim Yana mai cewa, sarrafa kayayyakin jabu na cikin abubuwan dake assasa gazawar cika ka’idar hukumar tabbatar da nagartar kamfanoni ta kasa
Inda ya ce hukumar za ta soke rajistar duk wani kamfani ko cibiyar sarrafa kayayyakin da suka yi satar sunan wani don aikata ba daidai ba.
Malam Farouk Sulaiman ya ce lamarin hakkin mallaka ba abu ne da hukumarsa za ta iya yaki da shi ita kadai ba, har sai sauran hukumomin da suke da ruwa da tsaki a fannin sun bada tasu gudunmawar.
You must be logged in to post a comment Login