Ƙetare
Za mu yi amfani da soji wajen dakile juyin mulkin da aka yi a Benin – Ecowas

Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ce ta shirya wajen taimaka wa Jamhuriyar Benin da sojoji domin daƙile juyin mulkin da wasu sojoji suka yi iƙirarin yi.
Matakin na Ecowas na zuwa ne bayan wani rukunin sojoji ya sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon a kafar talabijin ɗin ƙasar a yau Lahadi tare da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta ɗora wa sojojin alhakin “duk wani rai da aka rasa” sakamakon yunƙurin juyin mulkin nasu.
Sai dai hukumomi a ƙasar sun ce sun shawo kan lamurra bayan yunƙurin juyin mulkin.
You must be logged in to post a comment Login