Labarai
Za mu yi haɗin gwiwa da wani kamfani a Ghana domin aikin kwashe shara a Kano- Dr. Kabiru Getso
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta sake yin haɗin gwiwa da wani kamfanin mai zaman kan sa a kasar Ghana domin aikin kwashe shara da kuma sarrafa ta zuwa dukiya.
Kwamishinan Muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya sanar da hakan da yammacin ranar Talata, lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin kamfanin domin tattaunawa kan yadda za a ƙulla alaƙar tsakanin gwamnati da kamfanin.
Dakta Getso ya kuma ce za a yi haɗin gwiwa da kamfanin ne sakamakon yadda ya fi kamfanin da yake aikin kwashe shara yanzu haka a Kano da kayan aiki.
Ya ci gaba da cewa, gwamnatin za ta ci gaba da ayyuka da dukkanin kamfanonin domin aiki tare da gwamnatin jihar ba tare da ayyukan su sun yi karo da juna ba.
“Wannan kamfani na Ghana yana da manyan motocin aikin shara sama da dubu biyu, don haka ba za a hada da wannan kamfani da muke tare da shi yanzu haka ba, saboda su suna da motoci goma sha takwas ne ciki har da wanda gwamnati ta ba su” a cewar Getso.
Idan za a iya tunawa a bara ne gwamnatin jihar Kano ta yi hadin guiwa da wani kamfani mai zaman kan sa a nan Kano da zai riƙa sarrafa shara zuwa dukiya, har ma ta rushe hukumar kwashe shara ta REMASAB tare da damƙawa kamfanin ragamar aikin.
You must be logged in to post a comment Login