Labaran Wasanni
Za’a dawo gasar Bundesliga a watan Mayu
Shugaban hukumar kwallon kafar jamus (DFL) Christian Seifert, yace ana shirye shiryen dawowa gasar a farkon watan Maris, ba ‘yan kallo.
A baya dai an dage gasar ta kasar Jamus, rukuni na farko dana biyu har zuwa ranar 30 ga watan Afrilun bana sakamakon barkewar cutar Corona Virus.
Rahotanni dai sun tabbar da cewa zuwa yanzu kasar Jamus na daga cikin kasashen da suke kan gaba gaba wanda cutar tafi kamari a nahiyar Turai, da yawan mutane 110,000, da suka kamu da cutar in da zuwa yanzu haka mutum 2,100 suka rasu.
Labarai masu alaka.
Muller ya saka hannu a sabon kwantiragi da Bayern Munich
Cutar Corona ta sa an dakatar da ‘yan kallo shiga wajen wasanni
Christian Seifert ya kara dacewa nan ba da dadewa ba za’a dawo gasar, wanda hakan zai kara karsashi ga al’umma da debe musu kewa a wannan hali da ake ciki, kuma a shirye suke da su taimakawa gwamnati a kokarin ta na yakar cutar da kuma jin shawarwarin ta kan yadda gasar zata kasance.
Siefert, ya kara dacewa kammala gasar akan lokaci zai kar bada wata dama ta sanin inda aka dosa a kwallon kafar nahiyar Turai ba ma kasar Jamus ba, in da yace sauke gasar gaba daya zai jefe kungiyoyi guda biyar daga gasar a cikin mummunan hali na rashin kudi, wanda hakan ka iya ja wo wa kungiyoyin rushewa.
You must be logged in to post a comment Login