Labaran Wasanni
Za’a dawo gasar wasan Tennis ta US Open a bana ba tare da ƴan kallo ba
An kammala shirye shiryen dawowa gasar wasan Tennis na gasar US Open a watan Agustan bana ba tare da ‘yan kallo ba kamar yadda gwamnan birnin Newyork na kasar Amurka , Andrew Coumo ya tabbatar.
Bayan dogon hutun da a kayi a gasar sakamakon cutar Corona data dakatar da al’amurran wasanni , gwamna Coumo, ya tabbatar da cewar gasar da ake a Flushing Meadows, zata gudana ranar 31 ga watan Augusta zuwa 13 ga watan Satumba.
Coumo , ya kara dacewa hukumar Kwallon wasan Tennis ta Amurka, zata yi gagarumin shiri na ganin cewar an kula da lafiyar ‘yan wasa, masu lura dasu , zaman su a dakunan su da kuma yanayin zirga zirgar su.
‘Yan wasa da dama sun nuna rashin jin dadin su ,na tsare tsaren gudanar da gasar , inda zakaran gasar a yanzu haka ta ATP, Novak Djokovic, ya ce tsarin amfani da mutane dai -dai ga kowanne dan wasa Abu ne da ba zai yiwu ba.
Ya yin da shima Rafeal Nadal da ‘yar wasa Simona Helep wacce take zakarar Wimbledon ta mata , sai Ashleigh Barty , duk sun nuna rashin jin dadin ka’idojin da aka gindaya.
You must be logged in to post a comment Login