Labarai
Za’a daina dogaro akan Tumatirin kasashen waje
Kungiyar manoman Tumatir ta kasa ta ce nan ba da dadewa ba, kasar nan za ta daina dogara da Tumatirin da ake shigo da shi daga kasashen waje.
Shugaban kungiyar reshen jihar Kano Alhaji Sani Dalladi Yadakwari ne ya bayyana haka, yayin bikin rabon iri na zamani da aka rabawa manoman tumatir, a garin kadawa da ke yankin karamar hukumar Garun Malam a nan jihar Kano.
Ya ce, bikin rabon irin tumatirin da aka guidanar a yau, zai taimaka gaya wajen bunkasa noman tumatiri a jihar Kano.
Da ya ke nasa jawabin, Shugaban kamfanin tumatirin da ya yi rainon irin, Alhaji Abdulkadir Kaita, cewa ya yi, manoma dubu goma ne za su fara amfana ta cikin shirin a zangon farko.
Dangote: ya kafa kamfanin rainon irin timatiri a Kano
Wasu daga cikin manoman Tumatirin da suka amfana ta cikin shirin sun ce, za su yi amfani da irin da aka basu wajen bunkasa noman da su ke yi.
Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya ruwaito cewa, rabon irin wanda daya ne daga cikin shirin tallafawa manoma na Ancho Borrowers da babban bankin kasa CBN ke gudanarwa, ana saran manoman tumatir dubu dari ne za su amfana nan da shekara daya.