Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dangote: ya kafa kamfanin rainon irin timatiri a Kano

Published

on

Kamfanin sarrafa timatiri na Dangote ya kafa gidan rainon Tumatiri da kudin say a tasamma Naira biliyan 3 da ake kira da Green House Nursery anan Kano, wanda aka tsara zai dinga samar da tan na tumatiri da zai kai Naira miliyan dari  uku 300 zuwa miliyan dari uku da hamtsi

Manajan darakatan Kamfanin Abdulkarim Lawal Kaita ya bayyana hakan yana mai cewar kamfanin na Green House Nursery yace kafa kamfanin na sarrafa tumatiri na Dangote zai kara yawan iri da manoma za su yi amfani da shi wajen noman zamani da kuma na gargajiya a kasar nan.

Abdulkarim Lawal Kaita ya sheda cewar, kafin gwamnatin tarayya ta samar da yawan tumatirin da mutanen kasar za su amfani da shi a cikin gida da kuma fitar da shi zuwa kasashen waje, akwai bukatar a hana shigo da irin tumatire da kasashen waje mussaman ma idan kamfanin ya kafo.


A cewar sa, sabon binciken da kamfanin ya gudanar wajen samar da ingantaccen tumatire kamfanin zai dakile yunkurin gwamnatin tarayya na hana amfani da dala miliyan dari uku da Hamsi ta hanayar hana shigo da tumatirin da ak sarrafa daga kasashen wajen.

Manajan daraktan ya kara da cewar ‘yan Najeriya fiye da miliyan 2 suke amfani da tan din Timatirin da ake sarrfawa, amma kuma sabon kamfanin zai samar da tam miliyan 8 a duk shekara.

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!