Labarai
Za’a fara karatun hadaka tsakanin kwalejin horar aikin tsafta ta Kano da Burtaniya – Getso
Kwalejin horar da tsaftar muhalli ta Jihar Kano , School of Hygiene , zata fara karatun hadaka na sauyin Dalibai da Malamai daga makarantar aikin lafiya ta Burtaniya, da sauran wasu kasashen Ketare don bunkasa harkokin aikin lafiya.
Shugaban makarantar Dakta Bashir Bala Getso, ya bayyana haka a yau a taron manema labarai daya gudana a harabar makarantar a wani bangare na cikar wa’adin shekara daya na gudanar da mulkin sa a makarantar.
Dakta Bashir Bala Getso, ya kara dacewa a cikin shirye -shirye da makarantar ke yi karkashin jagorancin sa don magance matsalolin da ake dasu na harkokin kiwon lafiya, hukumar makarantar ta fito da sababbin darussa na kiwon lafiyar al’umma da za tayi hadaka da wasu jami’o’in kasar nan, a matakin karatu na Digiri.
Bashir Bala Getso, ya kuma ce tuni shiri ya yi nisa na hadaka da kwararru wajen , samar da ingantatun bayanai ga al’umma kan yadda zasu ke gudanar da rayuwar su cikin tsafta da cikakkiyar kiwon lafiya , musamman ma a kauyuka.
Wakilinmu Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa , shugaban makarantar ya ce tuni sun aike da kudiri na Neman majalisar jihar Kano, ta yi Doka ta daukar daliban makarantar aiki da zarar sun kammala karatun su, a kamfanunuwa masu zaman Kansu , da kasuwanni da ma’aikatun gwamnati , musamman ma wajen kula da lafiya da tsaftar waje, don rage rashin samun aikin yi ga Daliban.
You must be logged in to post a comment Login