Labarai
Za’a rufe daukan ma’aikatan wucin gadi – Keyamo
Gwamantin tarraya za ta rufe daukan ma’aikata na wucin gadi karkashin hukumar samar da aikin yi ta kasa, a ranar Ashirin da daya ga watan da muke ciki na Satumba.
Wannan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun daraktan Jeral na hukumar Malam Nasir Ladan.
A cewar sanarwar, hukumar za ta dauki ma’aikatan wucin gadin guda dubu dad-daya a kakanan hukumomi fadin kasar nan dari bakwai da saba’in da hudu.
Ta cikin sanarwar, hukumar ta bukaci masu sha’awar yin aikin da su tuntubi kwamitin da hukumar ta kafa wadanda ke da alhakkin daukan ma’aiktan.
Haka zaklika, hukumar ta ce duk wadanda suka samu nasara samun aikin za su biya Naira dubu Ashirin na tsawon watanni uku ta banki.
You must be logged in to post a comment Login