Manyan Labarai
Za’a sanyawa unguwannin ‘yan gayu na’ura mai amfani da hasken rana
Shugaban hukumar kula da Futilun kan titi da kayatasu na jihar Kano Injiniya Abdullahi Garba Ramat yace suna shirin canza tsarin wasu fitilun kan titinan jihar Kano da suke amfani da manyan injina zuwa na’ura mai amfani da hasken rana.
Injiya Garba Ramat ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wakilin Radio Freedom Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa dan gane da matsalar rashin wutar lantarki a titu nan jihar Kano.
Ibrahim Garba Ramat ya kara da cewa cikin titunan da suke shirin canjawa tsari zuwa na’ura mai amfani da hasken rana akwai Titin gidan Gwamnatin jihar Kano da kuma titunan cikin Unguwar Nasarawa saboda kula da tsaro.
Rubututtuka masu alaka:
Ramat: muna sauya fasalin yadda ake rarraba wutar fitilun Titunan Kano
Bamu rufe titin unguwar Dorayi ba – ‘Yansandan Kano
A cewar shugaban hukumar Ibrahim Garba Ramat yace dalilin da yasa suke bukatar titu nan da suke da tsaro sosai bai wuce tsoron kada bata gari su sace kayan ba, wanda hakan yasa suka fara tunanin irin wuraren da za suyi amfani da na’aurar saboda su samu tsaro sosai.
Garba Ramat ya kara da cewa ba ko ina zasu saka nau’ara mai amfani da hasken rana ba saboda gudun abunda ka iya faruwa akan su.