Labarai
Zabtarewar kasa ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 50 a Myanmar
Akalla mutane 50 ne suka mutu bayan zabtarewar kasa a wani wuri da ake hakar ma’adanai a arewacin Myanmar, a cewar hukumomin kaasr.
Lamarin wanda ya auku da safiyar ranar alhamis ya faru ne a yankin Hpakant da ke jihar Kachin bayan ruwan sama mai yawa, in ji ma’aikatar kashe gobara ta Myanmar.
Sanarwar ta ce, laka ta lullube masu hako ma’adanai, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 50.
Ma’aikatar ta ce har yanzu ana ci gaba da aikin ceto mutanen da kasa ta rufe, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Facebook.
Hotunan da aka sanya a shafin Facebook sun nuna yadda masu aikin ceto ke aikinsu cikin laka.
Zaizayewar kasa ko kuma laka ba sabon abu ne ba a yankin, na mutanen da ke fama da tsananin talauci yayin da suke neman abinda za su ci.
You must be logged in to post a comment Login