Labarai
Zamfara: Minista tsaron Najeriya ya yi karin haske kan kalamansa na baya
Ministan tsaron Najeriya Burgediya janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya ce, furicinsa na cewa wasu daga cikin masu rike da Masarautun Gargajiya a jihar Zamfara na taimakawa ‘yan ’bindiga ba ya yi bane da nufi cin mutuncin su.
Ministan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Kanal Tukur Gasau.
A cewar sanarwar, hankalin Ministan ya tashi ne biyo bayan yadda wasu kafafen yada labarai ke bayyana yadda ake zargin wasu masu rike da masarautun gargajiya a jihar da hannu cikin rikice-rikicen da ake samu a jihar ta Zamfara.
Haka kuma sanarwar ta kuma gargadi masu yada irin wadannan kalamai da suke kawo tinziri tsakanin al’umma da su guji yin hakan domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Rahotani sun bayyana cewa Ministan ya karbi rahotannin tsaro na sirri daban-daban kan matsalolin tsaro da ke abbar jihar ta Zamfara.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai Ministan tsaro Mansur Dan’Ali, ya ce, akwai wasu daga cikin masu rike da masarautun gargajiya a jihar ta Zamfara da ke taimakawa ‘yan bindiga.