Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Katsina – ‘yan Bijilanti sun kashe yan ta’adda biyu – ‘Yan sanda

Published

on

‘Yan kungiyar sa kai da aka fi sani da Vigilantee sun yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga biyu a kauyen ‘Yantara dake karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina bayan da suka kai hari kauyen a daren jiya Talata.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, yan bindigar sun kai hari kauyen ne da misalin karfe daya na daren jiya Talata, inda ya ce, daya daga cikin mazauna kauyen mai suna Mamman Dahiru dan shekara 30 ya rasa ransa sakamakon harin na su.

Gambo Isa ya kuma kara da cewa, yayin harin na ‘yan bindiga sun fatattaki mazauna yankin tare da kashe wasu daga cikin dabbobin su.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!