Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu ƙara ƙarfafa alaƙa da ƙasar Canada -Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ce zata karfafa dangantaka da kasar Canada ta fuskar ilimi da kiwon lafiya.

Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Canada James Christoff a ofishinsa.

Gwamnan Yusuf Ya godewa jakadan kasar Canada bisa tallafin da kasarsa take bawa al’umar jihar Kano a bangaren noman rani da yaki da zaizayar kasa da kwararowar hamada.

Da yake jawabi Ambassador ƙasar ta canada James Christoff ya bayyana maƙasudun ziyarar ta su.

Inda yace babbar alaƙa ce tsakanin su da jihar kano shiyasa sukazo domin ƙara ingantata wajen tallafa musu a fannonin noma lafiya.

Haka kuma gwamnatin kano ta nemi kasar ta canada da tallafa mata wajen samarwa da ƴan jihar kano guraben karatu a ƙasar ta Canada.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!