Labarai
Zamu ƙarawa limamai kuɗin Alawus ɗin da ake basu
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ƙarawa dukkan nin limaman masallatan juma’a kuɗin da ake basu a wata la’akari da yadda abin da ake biyan su yayi kaɗan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da limaman masallatan juma’a dake faɗin jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya ce la’akari da irin gudunmawar da limaman suke bayarwa ga addinin musulunci ya sanya gwamnatin jihar Kano zatayi wannan huɓɓasa wajen ƙara musu alawus ɗin da ake basu.
Haka zalika Gwamnan ya buƙaci malaman Addinin musuluncin da ke faɗin jihar kano da su mayar da hankali wajen faɗakar da al’umma abin da addini ya tanadar domin kawowa jihar kano ci gaba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma ce yawan faɗakar da al’umma da malamai sukeyi na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tarbiyyar al’umma.
Haka kuma gwamnan ya ce wannan ƙarin kuɗin da gwamnati zatayiwa limaman zaizo ne kai tsaye daga ofishin babban akantan kuɗi na jihar
Wasu daga cikin limaman masallatan juma’a dake nan kano sun wannan abu da gwamna zaiyi musu abin a yaba ne.
Wanda hakan zai ƙara karfafa musu gwiwa da ci gaba da gudanar da aikin su yadda ya kamata.
Haka kuma gwamnan ya ce yanzu haka ya sanya kwamitin da zai sanya idanu wajen kula da ciyarwar azimin watan Ramadana domin samarwa da al’umma sassaucin matsin da ake ciki.
You must be logged in to post a comment Login