Labarai
Zamu bada tallafin kayan abinci na N35,508 –NEMA
Hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, ta ce za ta fara rabon kayan abinci ga sansanoni yan gudun hijara a jihar barno da addadinsu ya kai Dubu talatin da biyar da dari biyar da takwas.
Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan hukumar Alhaji Mustapha Ahmed Habib.
inda ta ce zata fara rabon ne daga manyan sassanonin dake jihar da suka hadar da Jakana,Mainok, da kuma wasu Sansanonin dake fadin jihar.
Alhaji Mustapha Ahmed ya ce sun dauki gabarar rarraba abinci ga yan gudun hijarar dake fadin jihar duk wata domin ganin sun rage musu radadin da yake damunsu.
You must be logged in to post a comment Login