ilimi
Zamu bawa ilimi gudunmawa ta musamman a Jihar Kano
- Ba za muyi kasa a gwiwa ba, wajen ciyar da Ilimisu gaba, tare da Samar da kayyakakin koya da koyarwa.
- Alumma na samun ci gaba da ingantancen ilimi” ne kadai idan ana bawa ilimi fifiko a cikin al’umma’ inji Kwalli.
- Gwamnati ta ce zata za ta Kara jajircewa wajen samun ilimi da nufin inganta rayuwarsu.
Kungiyar tallafawa ilimin ‘ya’ya mata a Jihar Kano AGILE, ta ce, ba za ta Yi kasa a gwiwa ba, wajen ciyar da Ilimisu gaba, tare da Samar da kayyakakin koya da koyarwa ga malamai.
Sabon Shugaban kungiyar AGILE Malam Nasir Abdullahi Kwalli ne ya bayyana hakan a taron da kungiyar ta shirya a wani bangare na bikin ranar ilimi ta duniya.
Malam Nasir Abdullahi Kwalli ya ce” Alumma na samun ci gaba da ingantancen ilimi” ne kadai idan ana bawa ilimi fifiko a cikin al’umma’ inji Kwalli.
A nasa bangaren kwamishinan Ilimi na JIhar Kano Abdullahi Ya’u ‘yan-Shana, Wanda ya samu wakilcin Dakta Bello Shehu cewa ya yi ‘gwamnati a shirye take waje ganin ta inganta harkokin ilimi a Jihar Kano’.
Tare da cewa ” Jihar Kano za ta rubanya kokarinta da hadin gwiwar kungiyar AGILE don bunkasa Ilimi daliban JIhar Kano” A cewar ‘Yan Shana.
Wasu dalibai da suka hallarci taron sun nuna matukar farin ciki da wannan rana duba da muhimmcinta, tare da yin alkawarin cewa, za su Kara jajircewa wajen samun ilimi da nufin inganta rayuwarsu.
Rahoto:Aisha Muhammad ‘Yarleman
You must be logged in to post a comment Login